Labarai
Yan kasuwa a Nijeriya zasu fara amfani da Yuan kudin kasar Sin
Babban bankin kasa CBN ya ja hankalin masu safarar kayayyaki daga kasar china zuwa nan gida Najeriya dasu dinga amfani da kudin kasar ta china wato Yuan domin gudanar da harkar kasuwancin su a maimakon amfani da Dalar Amurka.
A cewar babban bankin hakan zai taimakawa kokarin da yake yi na bunkasa darajar naira a kasuwar musayar kudaden ketare da kuma kara darajar asusun ajiya na ketare.
A yanzu haka dai jami’ai daga babban bankin na CBN na tattaunawa da masu gudanar da kasuwanci a jihar Lagos da garin Aba da kuma wasu garuruwan a fadin kasar nan domin wayar da kan yan kasuwa muhimmancin amfani da Yuan din kafin bankin ya fara sayar dashi ga yan kasuwa a karshen wannan wata.
Rahotannin dai sun yi nuni da cewa a baya-bayan nan ne dai kasar nan ta samu matsalar karancin Dala Amurka sakamakon raguwar farashin danyan man fetur a kasuwar duniya tun a shekarar 2014.
Haka zalika a yanzu haka kasar nan ta samar da hanyoyin da dama da za su taimaka wajen musayar kudaden kasashen ketare daban-daban domin kaucewa yin amfani da dala ita kadai.