Labarai
‘Yan Najeriya mazauna ketare 684 ne suka kamu da corona a kasashen waje – BOSS
Gwamnatin tarayya ta ce kimanin ‘yan kasar nan 684 ne suka kamu da cutar corona a kasashen waje, yayin da dubu 13, 844 basa dauke da cutar, cikin adadin ‘yan kasar nan da aka dawo da su guda dubu 14, 906 wadanda suka makale a kasashen ketare sakamakon annobar corona.
Shugaban kwamitin yaki da cutar na gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan, lokacin da yake bada rahoto ga kwamitin yaki da cutar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, kwamitin ya lura da yadda matasa a kasar nan suka bada gudunmawa wajen yaki da cutar, a don haka abin a yaba ne matuka.
Boss Mustapha ya kara da cewa, fargabar da ake na yaduwar annobar a tsakanin al’umma ya ragu, sakamakon gudunmawar da kungiyoyin matasa ke yi na fito da dabarun wayar da akan al’umma.
Ta cikin jawabin nasa, Boss Mustapha ya ce, a yanzu kasar nan ta dawo da ‘yan asali kasar mazauna ketare su dubu 14, 906 tun bayan bullar annobar corona, wanda ya kawo kaso 80 na matafyan matasa ne.
You must be logged in to post a comment Login