Labarai
Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti domin dakile cutar Mashako

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin bincike da dakile cutar mashako wato “Diphtheria”, bayan rahotannin bullar cutar a wasu kananan hukumomin jihar.
Kwamitin wanda shugaban cibiyar dakile cutuka masu yaduwa KNCDC, Farfesa Muhammad Adamu Abbas, ke jagoranta, zai gudanar da cikakken bincike kan adadin wadanda suka kamu da cutar da kuma wadanda suka rasu.
kwamitin zai kuma karfafa tsarin sa ido da gano masu dauke da cutar, tare da tabbatar da cewa ana samun rahotanni daga kananan hukumomi a kullum.
Gwamnatin ta ce za a duba gibin da ke akwai wajen rigakafi, tare da kara wayar da kan jama’a kan muhimmancin yin rigakafin mashako.
Ta ce cibiyoyin da aka ware domin kula da masu fama da cutar sun samu magunguna da sauran kayan aikin lafiya da ake bukata.
Gwamnatin Kano ta bukaci al’umma, shugabannin gargajiya da na addini da su ba hukumomin lafiya cikakken hadin kai, musamman wajen kai rahoton duk wani mutum da ake zargin ya kamu da cutar cikin gaggawa.
You must be logged in to post a comment Login