Labarai
Yan Sandan Abuja na shirin tsaurara mataki kan masu karya dokokin hanya

Rundunar ’Yan Sandan Abuja za ta tsaurara mataki kan direbobin da aron hannu yayin tuƙi da sauran masu karya dokokin hanya.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da Jami’ar ta hulɗa da Jama’a SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan ’yan Sandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ya umarci jami’an Rundunar su tsaurara matakan tabbatar da bin dokokin hanya tare da kama wa da gurfanar da masu karya dokokin.
Ya kuma umarci jami’an su ƙara sintiri da sa ido a manyan tituna da wuraren cunkoson ababen hawa domin kama masu yi wa mutane fashi a irin waɗannan wurare.
Kwamishinan ya gargaɗi jami’an da za su gudanar da aikin kan karɓar kuɗi, cin zarafi ko tsoratar da jama’a, yana mai cewa duk wanda ya karya umarnin zai fuskanci matakin ladabtarwa.
You must be logged in to post a comment Login