Labarai
Kotu ta bada umarnin tsare Engr Idris Wada Sale a PCACC
Kotun Magistrate da ke zamanta a Kano ta sahalewa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ci gaba da tsare tsohon kwamishinan ayyuka a gwamnatin Ganduje, watau Injiniya Idris Wada Saleh kwanaki 12 masu zuwa, sakamakon zarginsa da almundahanar naira biliyan daya na aikin gyaran wasu tituna.
Mai shari’a Tijjani Sale Minjibir, ne ya ba da umarnin ci gaba da tsare tsohon shugaban hukumar gyaran titunan ta Kano KARMA, a bisa kama shi da kuma gurfanar da shi da hukumar ta Anti-Corruption ta yi.
Da fari dai lauyan hukumar Salisu Tahir, ya roki kotun da ta sahale musu ci gaba da rike tsoho kwamishinan na tsawon kwani 14, yayin da kuma lauyan wanda ake kara Mustafa Idris, ya bukaci kotun da ta ba da belinsa.
Mai shari’a Tijjani Sale Minjibir, ya dage sauraren karar zuwa ranar 14 ga watan nan na Yuli da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login