Labarai
Yan sanda sun tabbatar da kai hari ƙauye Binarri da ke Taraba

Rundunar Yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba, ta ce, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari ƙauye Binarri da ke karamar hukumar Karim Lamido, inda suka kashe aƙalla mutum 10, suka yi awon gaba da kayayyakin abinci daga shaguna tare da ƙona gidaje masu yawa.
Cikin hirarsa da BBC kakakin ‘yan sandan jihar Victor Mshelizah ya tabbatar cewa mutum 10 da aka gano gawarsu akwai harbin bindiga a jikinsu.
Ya ce an gano takwas daga cikin gawarwakin, 6 maza ne, biyu mata, kuma sun miƙa wasu ga ‘yan uwarsu domin yi musu jana’iza,”.
Jami’in ya ce sun ƙara gano gawarwakin wasu mutane 15 da suka nutse a kogi bayan kifewar kwalekwalensu.
Mshelizah ya ce ya zuwa yanzu sun girke ƙarin jami’ai a yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin mutane.
You must be logged in to post a comment Login