Labarai
Bauchi: Yan Sanda sun kama mutane 2 bisa zargin su da fashi da makami

Rundunar Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama mutane biyu bisa zargin su da fashi da makami da ƙwace wayoyin salula a birnin Bauchi, bayan wani hari da ya jikkata mutane biyu.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar Lahadi.
A ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2026, wasu mutane biyu daga Unguwar Mahaukata da Unguwar Kur sun kai ƙorafin cewa wasu mutane kusan tara ɗauke da adduna da sanduna sun kai musu hari da misalin ƙarfe 9:00 na dare, inda suka ƙwace wayoyin salula guda huɗu masu darajar ₦340,000 tare da jikkata su.
Rundunar ta ƙwato adda guda ɗaya da ake zargin an yi amfani da ita wajen harin, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargi da wayoyin da aka sace. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar domin ƙarin bincike
You must be logged in to post a comment Login