Labarai
Yan sandan Adamawa, sun cafke wani magidanci da ya kashe tsohuwar matarsa
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta kama wani magidanci mai suna Aminu Abubakar, dan shekaru 56, bisa zarginsa da dukan tsohuwar matarsa mai shekaru 38 da haihuwa wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ta .
Wanda ake zargin, mazaunin Lelewaji, ta karamar hukumar Yola ta Kudu ana zargin ya kashe Nana Fadimatu kwana guda kafin auren ta da sabon mijin da zata aura.
SP Suleiman Nguroje shi ne mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka cafke shi.
“Ya daki tsohuwar matar tasa ne sakamakon cewa yaji zata daura wani auren inda yanzu mun maida binciken zuwa babban sashin binciken manyan laifuka idan har yanzu anan ana tattara bayanai.”
You must be logged in to post a comment Login