Labarai
‘Yan ta’adda fiye da 400 sun mika wuya a Nassarawa – John Enenche
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su dari hudu da goma sun mika wuya ga rundunar sojojin kasar nan a jihar Nassarawa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa Manjo Janar john Enenche ya fitar, ta ce, mutane sun hada da mata da kananan yara kuma ‘yan kungiyar Darus Salam ne.
Manjo janar John Enenche ya kuma ce mutanen sun mika wuyar ne ga dakarun Operation Whirl Stroke wadanda aka turasu aikin tabbatar da tsaro a garin Uttu da ke yankin karamar hukumar Toto.
Haka zalika dakarun sun kuma kai samame wata masana’anta da ake hada abubuwan fashewa tare da kwato na’urar jefa rokoki da buhuhunan takin zamani da gurneti na gargajiya da sauran wasu makamai da dama.
You must be logged in to post a comment Login