Kaduna
Yanzu-yanzu: An soke hawan sallah a Zariya
Masarautar Zazzau ta ce, ta soke hawan ranar sallah, da kuma hawan
Daushe da aka saba yi duk shekara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da masarautar ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren masarautar, kuma sarkin Fulanin Zazzau Alhaji Barau Musa Aliyu.
Sanarwar ta ce, an soke dukkan wasu taruka da bukukuwan da ake yi yayin bikin sallah, domin dakile yaduwar cutar Corona.
Masarautar ta Zazzau, ta yi kira ga al’umma da su yi biyayya ga matakan kariya daga cutar Corona, wadanda suka hada da sanya takunkumin rufe baki da hanci, da yawaita wanke hannu da kuma kaucewar cunkoson jama’a.
A cikin sanarwar masarautar ta ce, Sarki da ‘yan majalisar sa, za su fito masallacin idi na Kofar Doka, dake Zariya da karfe 8:30 na safe a ranar sallah.
A gobe Jumu’a ne musulmai a fadin duniya ke gudanar da idin sallar layya ta wannan shekara.
You must be logged in to post a comment Login