Labaran Wasanni
Yanzu-yanzu: Barcelona ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta Ronald Koeman

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta Kori mai horar da ‘yan wasan ta Ronald Koeman.
Barcelona dai ta Kori mai horarwar ne biyo bayan rashin nasarar da ya yi a gasar Laligar kasar Spaniya da ci 1-0 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Rayo Vallecano.
Koeman dai ya jagoranci kungiyar ta Barcelona tsawon watanni 14.
Kungiyar dai ta samu maki 15 cikin wasanni 10 data buga a gasar ta Laliga.
Kuma ta yi rashin nasara wasanni 2 cikin 3 a gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League.
Yanzu dai kungiyar na matsayin ta 9 a teburin gasar Laligar kasar.
Shugaban kungiyar Joan Laporta, ne dai ya sanar da sallamar mai horarwar, Ronald Koeman bayan rashin nasarar da ya yi a hannun Rayo Vallecano da ci 1-0.
.
Barcelona dai ta Kori mai horarwar ne biyo bayan rashin nasarar da ya yi a gasar Laligar kasar Spaniya da ci 1-0 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Rayo Vallecano.
Koeman dai ya jagoranci kungiyar ta Barcelona tsawon watanni 14.
Kungiyar dai ta samu maki 15 cikin wasanni 10 data buga a gasar ta Laliga.
Kuma ta yi rashin nasara wasanni 2 cikin 3 a gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League.
Yanzu dai kungiyar na matsayin ta 9 a teburin gasar Laligar kasar.
- Shugaban kungiyar Joan Laporta, ne dai ya sanar da sallamar mai horarwar, Ronald Koeman bayan rashin nasarar da ya yi a hannun Rayo Vallecano da ci 1-0.
You must be logged in to post a comment Login