Coronavirus
Yanzu-yanzu: Coronavirus ta shiga Jigawa

Gwamnan jihar jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar yace an samu mutum na farko a jihar jigawa daya kamu da cutar COVID-19 a karamar hukumar Kazaure.
Gwamnan ya bayyana hakanne yau lahadi a fadar gwamnatin jigawa, yayin da yake ganawa da manema labarai.
Wakilin mu Aminu Umar Shuwajo ya rawaito mana cewa gwamna Badaru yace a sabo da haka karamar hukumar Kazaure za ta zamo kulle tun daga wannan rana ta Lahadi zuwa tsawon mako guda.
Kazalika gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga shugaban kasa Buhari a madadin al ummar jigawa kan rasuwar Abba Kyari.
You must be logged in to post a comment Login