Labarai
Yanzu-yanzu: Ganduje ya dakatar da zagayen Mauludi
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da gudanar da zagayen bikin Mauludi a faɗin jihar.
Mai baiwa gwamna shawara kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
An dakatar da zagayen ne sakamakon shawarwari da hukumomin tsaro suka bayar, a cewarsa.
Ya ce “Gwamnati na gudun abin da zai je ya zo, da ka iya haifar da rashin lafiya a Kano bayan shafe shekaru biyar muna zaman lafiya”
Sai dai ya ce, zagaye kaɗai aka hana, don haka al’umma su ci gaba da gudanar da bukukuwan Mauludi kamar yadda aka saba.
Labarai masu alaka:
Bukukuwan Mauludi sun kankama a Kano
Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi
Yaya al’ummar Kano suka karɓi wannan sanarwar?
Freedom Radio ta tuntuɓi Malam Sharu Sani Janbulo wanda ke cikin masu shirya zagayen, inda ya ce, tuni suka karɓi umarnin da hukumomi suka bayar.
“Hukumomi sun gana da mu, sun yi mana bayani game da barazanar tsaron da ake fuskanta kan gudanar da zagayen”
Me za ayi a madadin zagayen Mauludin?
Malam Sharu Sani ya shawarci jama’ar Kano da su yi amfani da lokacin wajen yin salati ga Annabi (s.a.w) tare da sada zumunci.
“Ɗacin baya barin mu, amma haƙuri zamu yi mu yi ta begen ma’aiki da yanke-yanke da anko da muka saba yi” a cewarsa.
You must be logged in to post a comment Login