Labarai
Yanzu -yanzu : Gwamnan Ekiti ya kamu da cutar Corona

Gwamnan jihar Ekiti Dr. Kayode Fayemi ya sanar da cewa ya kamu da cutar corona.
Hakan na cikin wata sanarwar ce da gwamnan ya wallafa a shafin sa na Twatter a yau Laraba.
A cewar Kayode Fayemi wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan ya ce shi ne karo na uku da aka yi masa gwajin cutar kuma a wannan karon sakamakon ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar ta covid-19.
Gwamnan na jihar Ekiti ta cikin sanarwar ya ce, tuni ya dauki matakin killace kansa tare da samun kulawar jami’an lafiya.
You must be logged in to post a comment Login