Labaran Wasanni
Yanzu-Yanzu Manchester United ta sallami mai horar da kungiyar Ole Gunnar Solskjaer

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami mai horar da kungiyar Ole Gunnar Solskjaer, bayan wani zaman gaggawa data gudanar a jiya sakamakon rashin nasara da kungiyar ta yi a hannun Watford da ci 4-1.
Hakan na cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a yau Lahadi 21 ga watan Nuwambar 2021 a shafinta na Internet.
Zuwa yanzu dai kungiyar bata bayyana sabon mai horarwar da zai maye gurbin Solskjaer ba.
You must be logged in to post a comment Login