Labarai
Yanzu-yanzu: NLC ta janye yajin aikin da ta shirya tsunduma yau a Kano
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Kano NLC ta janye yajin aikin data ƙudiri farawa daga ƙarfe goma sha biyu na daren yau.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Kwamred Najeeb Yasin ne ya bayyana hakan yayin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon ke ganawa da manema labarai a daren Laraba.
Najeeb Yasin ya ce, janye yajin aikin ya biyo bayan tattaunawar da ƙungiyoyin su ka yi da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
A cewar sa, Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da dawo da kuɗin ma’aikatan da aka yanke albashin su a watannin baya.
Ya ƙara da cewa, a watan da muke ciki na Afrilu ko watan Mayu mai kamawa Gwamnatin zata dawo da kuɗaɗen da ta yanke.
A cewar sa, Gwamnatin Kano ta ce bata buƙatar sake dawo da biyan mafi ƙarancin albashi na naira dubu goma sha takwas ga ma’aikatanta.
Saboda haka ƙungiyoyin suka yanke shawarar janye yajin aikin da suka ƙudiri farawa daga karfe goma sha biyu na daren Laraba bakwai ga watan Afrilu.
You must be logged in to post a comment Login