Labarai
Yara dubu 33 a Katsina za su koyi karatu ta rediyo da talabijin – Bankin Duniya
Gwamnatin Jihar katsina ta ce, akalla yara dubu talatin da uku ‘yan firamare da ke aji daya zuwa uku za su koyi karatu ta kafar talabijin da rediyo karklashin shirin da bankin duniya ya dauki nauyi.
Shugaban shirin na Arewacin kasar nan Umar Bello ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a jihar ta Katsina.
Ya ce duk da shirin koyarwar an zabi wasu daga cikin gidajen talabijin da rediyo ne amma duk da haka yaran sun fahimnci yadda ake furta kalmomi da kuma yin karatu na hausa da turanci.
Umar Bello ta cikin jawabin nasa ya ce, sun tsara koyarwa ta daban ta hanyar tura malamai guda 15 cikin unguwanni wanda kuma kowanne malami zai koyar da dalibai goma ne kacal.
You must be logged in to post a comment Login