Labarai
Yau Kotu ke cigaba da zaman sauraron ƙarar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar kan CBN
A yau ne kotun kolin Nigeriya ta ke ci gaba da zaman sauraron ƙarar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar da gwamnatin tarayya kan buƙatar ƙara wa’adin amfani da tsofaffin kuɗi.
A ranar 22 ga watan Febrairu ne, kotun ta ɗage zaman sauraron ƙarar har zuwa yau 3 ga watan Maris.
Tun da fari dai gwamnatin Nijeriya ta ayyana ranar 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 1,000, da 500, da kuma 200.
Sai dai daga baya shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ‘ya amince da ƙara wa’adin amfani da su zuwa ranar 10 ga watan Fabarairu’.
Sai a biyo mu a labaran mu na gaba don jin yadda zaman ya kasance.
Rahoton: Madeena Shesu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login