Labarai
Yawan masu dauke da cutar HIV a Bauchi ya sauka – Gwamnati
Gwamnatin jihar Bauchi ta ce adadin masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a jihar ya sauka daga kaso 6, da ake dasu a tun daga shekarar 2001 zuwa sifili da digo 4 a shekarar 2019.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aliyu Maigoro ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi ga me da matsayar jihar kan masu dauke da cutar, a wani bangare na bikin ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki da aka gudanar a jiya.
Maigoro ya ce, a yanzu haka mutane dubu ashirin da biyar da dari takwas da tara ne ke rayuwa da cutar a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi, cikin su kuwa mutum dubu ashirin da dari tara da sittin da daya suna samun kulawa daga cibiyoyin lafiya.
Cikin jawabin nasa, ya ce jihar za ta tabbatar da kowanne ma’aurata sun gudanar da gwaji kafin uare don dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login