Kiwon Lafiya
Yin bahaya a sarari na haifar da cutar Typoid, Kwalara, Atini – Likita
Wani likita da ke aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Dr. Abdullahi Isah Kauran Mata, ya ce, yin bahaya a sarari ko bainar jama’a, yana haifar da yaduwar cututtuka masu yawa.
Dr. Kauran Mata ya bayyana hakan ne yayin zantawa da wakiliyar freedom radio, Asma’u Uba Muhammad.
Ya ce, ana daukar cututtuka irinsu: zazzabin Typoid, Kwalara da cutar shan inna, har ma da attini sanadiyar yin bahaya a sarari ko bainar jama’a.
‘‘Lokacin damina idan an yi ruwan sama, ruwan kan dauki wadannan bahayar da aka yi, ya kaisu cikin gida, wasu lokutan ya tura su cikin rijiya ko kuma ruwan kan shiga cikin bututun mai da ya fashe saboda haka idan aka debi ruwan rijiya ko na famfo ana iya kamuwa da wadannan cututtuka matukar wanda ya yi bahayar yana dauke da su’’ a cewar likitan.
You must be logged in to post a comment Login