Labarai
Yin nasiha ya janyo an yanke hannun wani matashi a Kano
Likitoci a Kano sun yanke hannun wani matashi da aka yanka sanadiyyar zuwa yin nasiha da neman sulhu.
Rahotanni sun ce matashin Salisu Hussain ya gamu da wannan ibtila’i ne a lokacin da yaje yin nasiha ga wani matashi Abubakar Ayuba, kan ya daina ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a unguwar Fagge.
Freedom Radio ta iske Salisun a asibiti cikin mawuyacin hali a ranar Lahadi.
Ɗan uwansa Auwal Hussain ya yi ƙarin bayani a kai.
“Salisu ya je wajen Abubakar domin yayi masa faɗa kan rigimar da suke da wasu da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da ake zarginsa”.
“Shi ne yayi zuciya ya ciro wuƙa ya yanke shi a ƙasan hammata”. A cewar Auwal.
Yanzu haka likitoci a asibitin ƙashi na Dala sun yanke wa Salisun hannu saboda wajen ya ruɓe.
Mahaifiyar Auwal Malama Zulaihat Abubakar ta bayyanawa Freedom Radio alhininta kan lamarin.
Ta ce “Lafiya ƙalau muke zaune da iyayen Abubakar a unguwa amma ya yiwa Salisu wannan illa, kullum yarona cikin neman na kansa yake baya faɗa da kowa”.
Rahotanni sun ce tuni rundunar ƴan sandan Kano suka cafke wanda ake zargin inda suke ci gaba da bincike a kansa.
Sai dai a kafafen sada zumunta ana ta yaɗa rahoton cewa masu ƙwacen waya ne suka sare shi, abin da ƴan uwansa suka musanta.
You must be logged in to post a comment Login