Labarai
Yiwa kundin tsarin mulki karan tsaye shi ya haifar da juyin mulki a Mali – Kabiru Sufi
Masanin kimiyar siyasa na Kwalejin Share fagen shiga Jami’a na CAS ya ce yi wa kundin tsarin mulki karan-tsaye shi ya haifar da juyin mulki a kasar Mali.
Har ila yau, masanin ya danganta rikicin kasar Mali da matsalolin da suka taso daga rashin kula da bukatun jama’a musamman saboda irin taskun da ‘yan kasar suka samu kansu a ciki
Masanin kimiyyar siyasa na kwalejin share fagen shiga jami’a “CAS” Malam Kabiru Sufi ne bayyana hakan ta cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan tashar Freedom Rediyo da ya mai da hankali kan juyin mulki da aka gudanar a kasar Mali.
Sufi, ya kara da cewa, duk kasar da ta yiwa kundin tsarin mulkin ta karan tsaye to kuwa zai haifar da rikicin da zai zamo ya haifar da juyin mulki, kuma matukar aka gaza daukan mataki to wata kasar ma zata yi sha’awar aikatawa.
Ya kara da cewa rashin tsaro darashin adalci a kasar nan na kamanceceniya da abubuwan da suka haifar da rikicin kasar Mali, inda ya ce akwai bukatar mayar da hankali don kawo karshen sa.
Malam Kabiru Sufi ya tabbatar da cewa wannan juyin mulki na kasar Mali izina ce ga sauran kasashe, wanda idan basu gyara matsalolinsu ba, suma kasashensu na iya afkawa cikin wannan matsalar.
You must be logged in to post a comment Login