Labarai
Za a fara binciken hukumomi kan raba dai-dai tsakanin ‘yan kasa
Hukumar raba dai-dai ta kasa FCC ta ce nan gaba kadan ba da dadewa ba, za ta fara bin diddigin ma’aikata da ke ma’aikatu da hukumomi da kuma sassan gwamnati domin tabbatar da cewa ba a sabawa dokar raba dai-dai ba.
Shugabar hukumar, Dr Muheeba Dankaka ce ta bayyana haka, yayin wani taron manema labarai a ofishinta da ke Abuja.
Ta ce, hukumar za ta hukunta duk wata ma’aikata ko hukuma ko kuma sashe na gwamnati da ya nuna son kai wajen daukar ma’aikata ko ya yi wani abu da ya sabawa dokar raba daidai.
Dr. Muheeba ta ce, wani bangare na ayyukan hukumar da suka gano wanda ba a fiya bashi muhimmanci ba, shi ne tabbatar da cewa, anyi raba dai-dai wajen gudanar da ayyukan raya kasa da samar da abubuwan more rayuwa da gwamnati ke yi.
You must be logged in to post a comment Login