Coronavirus
Za a gina cibiyar gwajin Corona a Jigawa
Gwamnatin jihar jigawa tace tana aikin gina cibiyar gwajin cutar Coronavirus da zata fara aiki nan da makonni biyu masu zuwa.
Gwamnan jihar Alh. Muhd Abubakar ne ya sanar da haka ga manema Labarai da yammacin ranar talatar nan a gidan Gwamnatin jihar dake Dutse.
Gwamnan yace sun dauki wannan mataki ne sakamakon kalubalen da jihar ke fama dashi na rashin cibiyar gwaji wadda hakan ke janyo mata jinkirin gano masu dauke da cutar.
Karin labarai:
Uwargida ta haifi ‘yan hudu a Jigawa
Ma’aikatan lafiya sun kamu da Corona a Jigawa
Kazalika gwamna Badaru yace wannan cibiya za ayi mata matsugunni ne a wani sabon sashe dake cikin babban asibitin Dutse, wato Dutse (General Hospital).
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito gwamnan na cewa wannan cibiya koda bayan cutar Coronavirus, cibiyar za ta cigaba da gwajin cutuka irinsu Ebola da lassa da dai sauran cutuka masu yaduwa.
You must be logged in to post a comment Login