Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Za a kara samar da sabbin cibiyoyin killace masu Corona a Kano

Published

on

Gwammatin jihar Kano ta ce zata yi amfani da wasu wurare anan Kano don mayar dasu cibiyoyin killace masu fama da cutar Corona.

Mataimakin Gwamnan Kano kuma shugaban kwamitin kar ta kwana akan yaki da cutar Corona Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan a yau jumu’a lokacin da yake zagayawa wuraren da za’a mayar cibiyoyin.

Ya kara da cewa dalilin wannan yunkuri shi ne domin a samu wadatattun cibiyoyin killace masu cutar anan Kano duk kuwa da cewa sauran cibiyoyin har yanzu suna aiki.

Nasir Gawuna ya kara da cewa wuraren da za ayi amfani da su sun hada da asibitin Mafitsara na Abubakar Imam sai dakin karatu na Murtala Muhammad da kuma tsohon hotal din Daula.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa mataimakin Gwamnan Kano Nasir Yusuf Gawuna ya kuma shawarci alumma da su cigaba da bin shawarwarin jamian lafiya da kuma addu’ar kariya daga cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!