Labarai
Za a samar da cibiyar dawo da layukan da suka bata a kasar nan – NCC/NIMC
Gwamnatin Najeriya ta amince da samar da cibiyoyi domin dawo da layukan wayar da suka bata ko aka sace a kananan hukumomin kasar 774.
Hakan na cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin NCC da NIMC suka fitar.
An cimma wannan matsaya ne a zama na hudu na kwamitin ministoci kan rijistar katin dan kasa da layin waya.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana rijistar katin dan kasa ta NIN da akan iya yi a kan waya an kara tsawaita ta daga shekara daya zuwa shekara biyar.
You must be logged in to post a comment Login