Labarai
Za mu rage wa maniyyata naira 500,000 a kudin da za su cika- gwanatin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta baiwa Alhazan da suka biya kudin aikin Hajjin su a baya kyautar naira dubu dari biyar – biyar domin su sami damar biyan ragowar kudin da hukumar NAHCON ta kara na kudin aikin Hajjin bana.
Darakta Janar na hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Kano Alhaji Lamin Rabiu Dan Baffa ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a yau Laraba.
Alhaji Lamin Rabiu yace gwamna Abba Kabir yayi la’akari ne da irin yadda maniyyata suka sakankance sun kammala biyan kudin su na aikin Hajji, amma rana tsaka NAHCON ta sanarda karin kudin kujerar aikin Hajjin na bana.
A cewarsa kyautar kudin da gwamnan ya yiwa maniyyatan kimanin biliyan daya da miliyan dari hudu ya shafi iya maniyyatan da suka biya kudadensu ne a baya a hukumar banda sabbi masu biya a nan gaba.
hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON data roki hukumar kula da aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudi Arabia data kara wa’adin da aka sanya za’a rufe karbar kudin kujerar aikin Hajjin bana wato a daren gobe Alhamis 28 ga watan da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login