Coronavirus
Za’a ci gaba da gwajin cutar Corona a Kano
A yau Asabar Asibitin Aminu Kano ya rufe sashin da ake gwajin cutar Covid-19 a jihar Kano sakamakon feshin maganin kashe kwayoyin cutuka da akai a gurin.
Shugaban sashin gwajin Cutar Corona a Asibitin Aminu Kano Dakta Nasiru Magaji Sadik ne ya bayyna hakan a zantawar sa da mai Magana da yawun Asibitin Hajiya Hauwa Muhammad, game da dalilan da suka sanya aka rufe bangaren.
AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu
Dakta Nasiru Magaji ya kuma ce sun rufe gurin ne sanadiyyar feshin kasha kwayoyin cutuka da akai, wanda kuma zai dauki akalla awanni arba’in da takwas kafin a ci gaba da amfani da gurin.
Ya kuma ce da zarar lokacin da aka dibawa wajen da aka gudanar da feshin ya cika za’a ci gaba da gwada mutanan da ake zargin na dauke da cutar ta Covid-19.
A ziyarar da Freedom Radiyo ta gudanar a Asibitin na Aminu Kano ta lura cewa babu kowa a gurin da ake gudanar da gwajin cutar ta Covid-19 inda gurin ya kasance a kulle.
You must be logged in to post a comment Login