Labaran Wasanni
Za’a fara gasar wasannin motsa jiki ta makarantun sakandare a Najeriya

A ƙalla makarantun Sakandire na gwamnati da masu zaman kansu 377 ne suka shiga wata gasa wacce wani banki ya san yawa makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin Tarayyar kasar nan, da jihar Delta za ta karbi bakunci.
Gasar wacce za’a fara a yau Alhamis 30 ga watan Satumbar shekarar 2021, gasa ce wacce bankin ya ke sawa a duk shekara ga makarantun.
A nasaran ministan matasa da wasanni sunday Dare zai kasance a wajen bikin bude gasar kana shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Amaju Pinnick zai halarci bikin bude gasar.
Kwamitin gudanar da gasar ya ce ya shirya tsab domin fara wasan a gobe.
You must be logged in to post a comment Login