Manyan Labarai
Za’a fara rage cunkoso a gidajen gyara hali – Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce ta fara wani shirin rage cunkoso a gidajen gyaran hali ta hanyar sakin kananan yaran da ke tsare a wannan lokaci na annobar korona da ma bayanta.
Ministan shari’ah na Nijeriya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka yayin wani taro ta intanet kan yin afuwa da rage cunkoson yaran da a ka hana wa ‘yanci a ƙasar.
Tun farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya kafa kwamitin da zai duba yiwuwar rage cunkoson ƙananan yara a gidajen yarin ƙasar, da kuma yin gyaran fuska kan aikace-aikacen gidajen yarin.
Daga cikin wadanda za su ci gajiyar shirin sun haɗa da wadanda shekarun da a ka yanke musu tuni sun ci adadi mai yawa, da kuma matan da ke zaman gidan yari tare da ‘ya’yansu da a ke tsoron za su iya kamuwa da cutar Korona.
You must be logged in to post a comment Login