Coronavirus
Za’a fuskanci farin abinci a jihohin Kano da Lagos – NBS
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce karancin abinci zai karu a jihohin Lagos da Kano da Abuja da kuma Jihar Rivers sakamakon cutar Corona.
Hakan a cikin rahoton da hukumar ta fitar a jiya Litinin tana mai bayyana cewa jihohin hudu su ne za su fuskanci karancin abinci sakamakon illolin da cutar Corona tayi.
Ta cikin rahoton hukumar, ta ce jihohin Abuja da Rivers wadanda kaso saba’in da biyu na al’ummar su basa iya cin abinci sau uku a rana tun farkon bullar cutar Corona zuwa yanzu.
NBS ta kuma bayyana cewa adadin mutanen da ke sanya kan su a kangin bauta ya karo a kaso biyu na wannan shekara sama da watan Yuni da Yuli da kuma kafin bullar cutar Corona.
Yayin da hukumar ta ce adadin ma’aikata a birnin tarayya Abuja ya ragu da kaso sha hudu, yayin da a jijojin Kano da River al’ummar cikin su ke gudanar da ayyukan noma da masana’antu fiye da kafin bullar Corona a kasar nan.
NBS ta cikin rahoton ta ce a yanzu al’ummar kasar nan na fuskantar rayuwa cikin kangin bauta fiye da shekarar 2018 da 2019
You must be logged in to post a comment Login