Manyan Labarai
Ganduje zai yi wa ‘yan takarar kananan hukumomi gwajin ta’ammali da miyagun kwayoyi
Gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar da yiwa ‘yan takarar da za su tsaya zaben kananan hukumomi gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin gudanar da zaben shugabanin kananan hukumomi a badi.
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan yau Talata wanda ya samu wakilcin Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a wajen taron wayar da kan ma’aikatan kananan hukumomi kan hanyoyin dakile sha da safarar miyagun kwayoyi.
Murtala Sule Garo ya ce nan gaba kadan gwamnatin Kano zata yi hadin gwiwa da hukumar hana sha da fataucin migayagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano NDLEA wajen yi wa dukkannin ma’aikatan gwamnati gwajin ko suna ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Wakilin mu Abba Isa Muyhammad ya rawaito cewa daga cikin wadanda suka halacci taron akwai ma’aikatan kananan hukumomi da kuma masu ruwa da tsaki.
You must be logged in to post a comment Login