Kiwon Lafiya
Zabe:Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta kama mutum 52 da zargin tashin-hankali
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta kama mutum 52 da ta zarge sun haddasa tashin-hankali a ranar 9 ga watan da muke ciki na Maris wanda aka gudanar da zaben gwamna da ‘yan majalisu a fadin kasar nan.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Hakeem Busari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Lokoja, yana mai cewa, yawancin wadanda suka kama, sun kama sune a ranar da aka gudanar da zabe gwamnoni da ‘yan makalisu, wanda ake zargin sun sace akwatin zabe tare haddasa tashin hankali.
Hakeem Busari ya kara da cewa, wadanda suka kama sun hada da Segun Olu da Yakubu Zakari da Salifu Mohammed Ajeshola Michael da Sabiu Halidu da Adamu Idris da Ojoma Eugene da Sunday Abuda Isaac Edoh da Joshua Ejibo da Ojogo Alhaji da kuma Monday Amodu.
A cewar kwamishinan an kama Segun Olu sakamakon harbin daya daga cikin ma’aikatan hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa INEC da kuma guda daga cikin masu kada kuri’a wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe a yankin Egbe da ke karamar hukumar Yagba ta yamma.
Hakeem Busari ya kuma ce, a wadanda aka kama din 12 daga cikin ‘yan zauna garin banza ne yayin sauran Arba’in din an kama sune bisa zargin su da sace mutane da kuma satar shanu hadi da bangar siyasa.