Labarai
Gwamnatin Zamfara ta musanta ciyo bashin fiye da biliyan 14
Gwamnatin jihar Zamfara, ta musanta ciyo bashin kuɗi sama da naira biliyan 14, inda ta ce kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo na naira biliyan 20.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnati ba ta ci wani bashi a gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.
A makon jiya ne hukumar kula da basuka ta kasa DMO ta fitar da rahoto game da gwamnonin da suka ci bashi a cikin wata shida.
Rahoton ya ce sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar, bayan rantsar da su a watan Mayun 2023.
You must be logged in to post a comment Login