Labaran Wasanni
Kano : Zamu ciyar da harkokin wasanni gaba – sabon shugaban SWAN
Sabon shugaban kungiyar marubuta wasanni ta jihar Kano SWAN Zaharadeen Sale, ya ce zai dora a inda shugaban daya sauka ya bari.
Zaharadeen Sale Ya kuma ce zai aiki kafada da kafada da tsofaffun shugabannin kungiyar da suka sauka ta yadda za’a bunkasa harkokin wasanni a Najeriya dama jihar Kano baki daya.
Zaharadeen Sale, ya kuma nuna godiyar sa ga mataimakinn shugaban kungiyar na kasa Lurwanu Idris Malikawa Garu bisa jajircewar da ya nuna na ganin an gudanar da zaben sababbun shugabannin kungiyar cikin nasara yadda ya kamata.
Da yake jawabi bayan rantsar da shugabannin kungiyar, mataimakin shugaban ta na kasa kuma kakakin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Lurwani Idris Malikawa Garu ya ce za su shigarwa da gwamnatin kano kudurori da suka hadar da gyaran filayan wasanni da inganta su tare da kirkirar wasu don inganta wasanni yadda ya kamata.
An dai gudanar da zaben sabbin shugabannin kungiyar a cibiyar ‘yan jaridu ta Kano wato Press center.
A Yau Talata ne dai 13/10 /2020 aka rantsar da sabbin shugabannin Kungiyar Marubata wasanni ta kasa reshen jihar Kano.
Ga Jerin Sabbin shugabannin kungiyar da aka rantsar.
1.Zahradeen Sale daya fito daga (Radio Nigeria pyramid ) a matsayin shugaba.
2.Abdulgafar Olawale Oladimeji daga (judicial sketch online Newspaper) a matsayin Sakatare
3.Aminu Halilu Tudun wada daga ( Freedom Radio ) a matsayin
Mataimakin Sakatare
4.Tukur Garba Arab daga (Voice of Nigeria) a matsayin ma’ajin kungiya
5.Abubakar Muhammad jibril daga ( guarantee Radio ) a matsayin
Sakataren harkokin kudi
6.Mubarak Ismail Abubakar daga (ARTV ) a matsayin jami’in walwalar jama’a.
You must be logged in to post a comment Login