Labarai
Zamu fara kama motocin gidan gwamnati muddin suka gaza biyan kudin haraji -KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta bukaci gwamnatin jihar Kano da sauran jam’iyyun siyasa dasu fara kokarin biyan kudin hajarin lika hotunan ‘yan siyasa na jikin motocin da ake sanya wa
Baffa Babba Dangundi ya bayyana hakan ne, lokacin da yake karbar bakuncin wasu kungiyoyin direbobin Adaidaita sahu da suka kawo masa ziyara domin nuna goyan bayansu da sabon tsarin yin rijasta domin tsaftace harkar sana’ar tuka adaidaita Sahu a Kano.
Haka zalika,Baffa Babba Danagundi ya kara da cewa matukar aka shiga sabuwar shekara kuma majalisar jihar Kano suka amince da kafa dokar shakka babu duk wanda ya lika kowane irin hoto a babur dinsa wajibi ne ya biya kudin haraji a hukumar KAROTA.
Mun fara aiki kan masu Keke da babura -KAROTA
An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA
Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda
Wakilin mu Abdulkarim Muhammd Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa, Shugaban Hukumar ta Karota Baffa Babba yace baza su saurarawa duk wanda bai yi sabuwar rijistar ba, za su dauki mataki mai tsauri akan duk wanda ya gaza yin rijistar.