Labaran Kano
Zamu kara tabbatar da zaman lafiya a Kano – Kwamishina

Sabon kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ce, zasu fito da sabbin dabaru domin ganin zaman lafiya ya kara tabbata a jihar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kawo fadar gwamnatin Kano daidai lokacin da ake gudanar da taron majalisar zartarwa a yau Laraba.
Ya kuma sha alwashin yaki da masu son tada zaune tsaye don kakkabe ire-irensu a fadin jihar.
“Ba zan dauki wani bangare kuma in kyale wani ba a ayyuka na, tabbatar da zaman lafiya da tsaro shine manufata a jihar Kano,” inji Kwamishinan.
You must be logged in to post a comment Login