Labarai
Zauren kare kima na Kano na goyan bayan kirkiro masarautu hudu
Zauren kare kima da cigaban Kano na goyan bayan kirkiro masarautu hudu
Zauren kare kima da cigaban Kano ya jaddada goyon bayansa bisa dokar kirkiro masarautu hudu da gwamnatin Kano tayi a baya-bayan nan.
Shugaban kungiyar Farfesa Abdu Salihi ne ya bayyana hakan, yayin taron ganawa da manema labarai a sakatariyar ‘yan jaridu.
Ya ce hakika tsarin kirkiro masarautu abu ne da zai haifar da alherai da ci gaban al’umma dake zaune a yankunan da wadannan masarautu suke.
Farfesa Abdu Saihi ya kara da cewa, galibi wadanda suke nuna rashin dacewar hakan suna yi ne bisa dalilai na kashin kansu, ba don al’ummar jihar Kano ba.
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito zauren kare kima da ci gaban Kano sun bukaci sauran masarautun hudun da aka kirkiro a baya-bayan nan da su baiwa Shugaban majalisar Sarakunan Kano Muhammadu Sanusi na biyu goyon baya wajen tabbatar da cigaban yankunan su da jihar Kano gaba daya.