Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ziyarar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo a Kano

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar aiki jihar Kano a ranar Alhamis ɗin nan.

Ziyarar ta shugaba Buhari ta ƙunshi ƙaddamar da aikin layin dogo daga Kano zuwa jihar Kaduna, da kuma Lagos zuwa Kano.

Buhari, ya sauka a filin taron da aka shirya gudanarwa a Zawaciki da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, daura da tashar Tsandauri ta Ruwa ta Dala Inland Dry Port.

Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar shugaba Buhari, ya ce aikin na daga cikin ƙudurorin gwamnatin sa na farfadowa tare da cike giɓin da ake da shi na harkar sufurin jirgin ƙasa a fadin ƙasar nan.

A cewar shugaban Layin-Dogon, zai taimaka wajen harkokin kasuwanci tsakanin jihohin kudancin ƙasar nan da Arewaci, musamman ma cibiyoyin kasuwancin wato Kano da Lagos.

Haka zalika shugaba  Buhari, ya ce aikin da zarar an kammala shi zai taimaka wajen rage yawan fasinjojin da suke amfani da motoci don yin zirga-zirga tsakanin jihohi, kasancewar zai haɗe, jihohin Lagos, Ogun, Osun Kogi ,Niger, Abuja da kuma Kaduna, har zuwa jamhuriyar Nijar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!