Connect with us

Labarai

Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da fara tura ruwa daga Goron Dutse

Published

on

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da sakin ruwan sha nan ta ke zuwa kwaryar birnin Kano.

 

Wannan na zuwa ne yayin ziyarar da Gwamnan ya kai ma’ajiyar ruwa ta saman Goron Dutse yayin ake dab da kammala aikin gyaran ta da zata dinga tarawa da tura ruwa zuwa kwaryar birnin Kano da adadin sa ya haura Lita Miliyan Arba’in.

 

A jawabinsa, Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa Muhalli da Sauyin Yanayi Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya ce Gwamnati ta samu nasarar kammala aikin a kan lokaci da ta yi al’kawari tun da fari.

 

Kwamishinan ya kuma ce za a bayar da layukan waya na kar ta Kwana ga jama’a domin sanar da ma’aikatar Ruwa wuraren da aka samu wata matsala da ke da alaka da gyaran hanyoyin ruwan sha a cikin gari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!