Connect with us

Labarai

Ƙungiyar Likitoci masu neman Ƙwarewa ta yi barazanar shiga yajin aiki

Published

on

Ƙungiyar Likitocin  masu neman Ƙwarewa a kasar nan, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako biyu ta biya buƙatunsu da suka shafi walwala da kuma ci gaban aikinsu, ko kuma su ɗauki matakin fara yajin aiki.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a yayin taronta na shekara-shekara karo na 46 da aka gudanar a jiya Lahadi a birnin Calabar, jihar Cross River, inda ta nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da yarjejeniyoyin da ta cimma da gwamnatin tarayya.

NARD ta ce buƙatunta sun haɗa da ƙarin albashi da alawus-alawus, inganta damar samun karin girma a aiki, rage yawan aiki da ya wuce kima, da kuma ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya domin rage ƙarancin likitoci a asibitoci.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a biya likitocin kuɗin ƙarin aikin da suke yi sakamakon ƙarancin ma’aikata, tare da ɗaukar matakan kare ma’aikatan lafiya daga hare-hare da kuma magance ƙaurar likitoci zuwa ƙasashen waje.

 

AMGD

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!