Labarai
Ƴan Dorayi sun kai ƙara hukumar tace fina-finai ka yunƙurin gina Film House

Al’ummar unguwar Dorayi Ƙarama da maƙwabtanta sun miƙa ƙorafi ga Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, inda suka bayyana rashin amincewarsu da shirin samar da Film House a yankin.
Hakan na zuwa ne bayan wani zama na musamman da ƙungiyoyin ci gaban yankin suka gudanar, waɗanda suka haɗa da Centre for Community Support and Human Development, Gidauniyar Mata Musulmi ta Kano, Community Build and Raise Initiative Hub, Arewa Mu Tashi Mu Farka da kuma Danfodiyo Islamic Center, tare da haɗin gwiwar dattawa, masu gidaje, limamai da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.
Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin, ɗaya daga cikin dattawan Dorayi, Dakta Yusif Ibrahim, ya bayyana damuwa kan yiwuwar tasirin aikin ga tsaro, zaman lafiyar mazauna yankin da kuma tarbiyyar matasa, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen tsaro da yankin ya fuskanta a baya.
Kungiyoyin da mazauna yankin sun ce sun kuma miƙa kwafin ƙorafin nasu ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Hukumar DSS, Hukumar Hisbah, Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano, Ma’aikatar Shari’a, Majalisar Malamai da kuma Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, tare da sauran hukumomin da abin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login