Connect with us

Labarai

Kaduna: Rundunar Ƴan sanda ta yi martani kan kisan Ummulkhairi

Published

on

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke cewa DPO na Marabar Jos, ASP Abdullahi S. Fakai, ya miƙa wata mata mai suna Ummulkairi da ake zargi da satar ƙananan yara ga wasu fusatattun matasa da suka kona ta.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansur Hassan, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda ne suka fara ceto matar daga hannun jama’a, kuma sun yi iya ƙoƙarinsu wajen kare rayuwarta kafin lamarin ya munana.

Ya kuma ce, zargin da ake yi wa jami’an ’yan sanda ba gaskiya ba ne, yana mai cewa wasu daga cikin shugabannin al’umma ma sun yi ƙoƙarin taimakawa wajen ceton matar.

DSP Mansur ya ƙara da cewa abin da ya faru ya samo asali ne daga matakin da wasu fusatattun matasa suka ɗauka, yana mai zargin cewa wasu mazauna yankin na ƙoƙarin kau da laifi daga kansu ta hanyar ɗora alhakin kan jami’an tsaro.

Rundunar ta jaddada cewa tana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano duk waɗanda ke da hannu a aika-aika tare da tabbatar da an hukunta su bisa tanadi doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!