Labaran Wasanni
2020 Olympics: D’Tigers ta gayyaci manyan ‘yan wasan NBA 12
Mai horas da kungiyar kwallon Kwando ta Najeriya D’Tigers, ya gayyaci manyan ‘yan wasan NBA 12 da za su shiga cikin tawagar ‘yan wasa 49 wadanda zasu wakilci kasar nan a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya.
Za dai a fara gasar ne mai taken Tokyo 2020 a watan Yulin 2021 mai kamawa a birnin Tokyo dake kasar Japan.
Tawagar kungiyar ta maza ta bude sansanin karbar horo a birnin California dake kasar Amurka.
‘Yan wasan sun hadar da: Monte Morris da Miye Oni da OG Anunoby da KZ Okpala da Precious Achiuwa da Udoka Azubuike da kuma Jahlil Okafor.
Sauran sune: Josh Okogie da Gabe Vincent da Al-Farouq Aminu da Jordan Nwora da Chimezie Metu da Ike Diogu da Festus Ezeli da Ike Iroegbu da Obi Emegano da Ike Nwamu da kuma Michael Gbinije.
You must be logged in to post a comment Login