Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

CAF ta saka ranakun wasannin neman shiga gasar mata ta matasa

Published

on

 

Hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF, ta saka ranakun da za ayi wasannin neman cancantar shiga gasar kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 20, da ‘yan 17.

Ranakun da aka saka na matasan ‘yan 17, sun hada da zagayeb farko daga 30 ga watan Oktoba zuwa Nuwamba 1 ga wata.

Za a yi zagaye na biyu daga Nuwamba 20 zuwa 21 ga wata.

Labarai masu Alaka

DA DUMI-DUMI: Sadio Mane ya lasher kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afrika

Kasar Guinea bata shirya fafatawa da Nigeria ba

Wasannin da za fafata sun hada da.

Nigeria da Ghana.
South Africa da Morocco.
Uganda da Cameroon.

Sai wasannin ‘yan kasa da shekaru 20.

Da za ayi daga 3 ga wata zuwa 5 na Satumba.Zagaye na biyu kuma daga 10 zuwa 12 ga watan Satumba.

Kasashen da zasu fafata sun hada da.

Morocco da Algeria.
Gabon da Congo.
Liberia da Cameroon .
Burkina Faso da Najeriya.
Senegal da Tanzania.
Ethiopia da Zimbabwe.
Botswana da South Africa.

Za ayi zagaye na biyu wato Second round ga kasashen da suka ci wasannin zagayen farko a watan Oktoba.

Daga ranakun 1 zuwa 2, zagaye na biyu daga ranar 8 zuwa 9 ga watan na Oktoba.

Sai zagaye na uku wato Third round .

Ranakun 5 zuwa 7 ,ya yinda zagaye na biyu zai kasance 12 zuwa 14 duk a watan Nuwamba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!