Labaran Kano
2023: Tsohon shugaban majalisar dokokin Kano Alhassan Rurum ya fice daga APC
Tsohon shugaban majalisar dokokin na jihar Kano kuma shugaban fansho na majalisar tarayya Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da ficewa daga jami’iyyar APC.
Rurum ya bayyana ficewarsa ne a zantawarsa da wakilin Freedom Radio Adam Sulaiman Muhammad a ranar Lahadi 8 ga Mayun 2023.
Alhassan Rurum wanda shine dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure ya ce daukar matakin ya zeno bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na yankin da yake wakilta.
Sai ya ce zai sanar da inda zai koma a nan gaba domin ci gaba shirin tunkarar zaben shekarar 2023 da ke karatowa.
Wanda yan siyasa da dama ke sauyin Sheka daga wannan jami’iyyar zuwa wata duka dai domin samun makoma.
You must be logged in to post a comment Login