Labarai
Uwar jam’iyyar PDP ta yi magana bayan korar Kwankwaso
Uwar jam’iyyar PDP ta ƙasa ta amince da shugabancin jam’iyyar a Kano na tsagin tsohon gwamna Kwankwaso.
Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa Kola Ologbondiyan ya fitar.
A cikin sanarwar ya ce, kwamitin ayyuka na jam’iyyar shi ne ya sanya idanu kan zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar wanda tsagin Kwankwaso ya samu kafa shugabanci.
A cewarsa, Shehu Wada Sagagi da sauran shugabanni da aka zaɓa lokaci guda, su ne halastattun shugabannin jam’iyyar a Kano, wanda za su shafe shekara huɗu a kan mulki.
Karin labarai:
Siyasar Kano: Dalilan korar Kwankwaso daga PDP
Siyasar Kano: An ja layi tsakanin Sha’aban da Ganduje
Hakan dai ya biyo bayan zaɓen da tsagin Aminu Wali suka yi a ranar Alhamis inda suka zaɓi sabon shugabanci ƙarƙashin Muhamminna Baƙo Lamiɗo.
Bayan nan kuma suka sanar da korar tsohon gwamna Kwankwaso.
Dama dai tun a Alhamis ɗin tsagin Kwankwaso su ka yi watsi da batun korar ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar na Kano Bashir Sanata.
You must be logged in to post a comment Login