Connect with us

Labaran Kano

Gwamnan Kano ya zabi Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin sa

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Alhaji Murtala Sule Garo zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Hakan na cikin wata sanarwar da Sakataren Yada Labaran gwamnan, Malam Mustapha Muhammad ya fitar a tsakar daren yau Laraba 22 ga watan Afrilu 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa zabar matakin ya yi daidai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya ba gwamna damar nada mataimaki idan an samu gurbi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa kujerar ta zama babu kowa ne bayan murabus din da tsohon mataimakin gwamna, Comrade Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris 2026.

Murtala Sule Garo mai shekaru 48 ya taba rike mukamai daban-daban a gwamnati da siyasa, ciki har da kwamishina baya ga shugaban karamar hukuma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!