Labarai
Gwamnatin Kano ta gudanar da daurin auren gata na mutane 3000

Gwamnatin Kano ta gudanar da ɗaurin auren zawarawa 3,000 ƙarƙashin shirin ta na auren gata, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance waliyyin malam Haruna Bashir, wanda aka yiwa iyalan sa kisan gilla watannin baya a yankin Chiranci da ke unguwar Ɗorayi.
Auren na Malam Haruna da amaryar sa Nabila Kabiru Yunusa da sauran amare da angwayen, wanda ya gudana a fadar Sarkin Kano, Gwamna Abba Kabir ne ya zamo waliyyin angwaye yayin da Sarki Muhammad Sunusi na II ya zamo waliyyin amare.
Da yake jawabi a wajen ɗaurin auren, babban Kwamandan hukumar Hisba ta Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ɗaurin auren ya gudana ne lokaci ɗaya da na sauran dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda ƙarƙashin shirin, gwamnatin Kano ta bai wa kowace amarya naira dubu 100 a matsayin sadaki da naira dubu 100 a matsayin tallafin fara sana’a.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce gwamnatin Kano ta ɗauki matakai da dama domin tallafawa Haruna Bashir, ciki har da ɗaukar nauyin aikin Umrah da Hajjin sa, tare da ba shi gida a Amana City domin taimaka masa ya farfaɗo daga ibtila’in da ya fuskanta.
Yayin gudanar da daurin auren babban kwamandan Hisbah Sheikh Daurawa yayi kira ga sabbin ma’auratan da su gina zamantakewar aurensu bisa fahimtar juna, zaman lafiya da haƙuri da juna domin samun zuri’a dayyiba.
You must be logged in to post a comment Login