Connect with us

Labarai

Shugabannin Yarbawa a Arewa sun bukaci Tinubu ya kara kaimi wajen rage talauci

Published

on

Kungiyar sarakunan Yarbawa da shugabanninsu da ke zaune a jihohin Arewa 19 da Abuja, ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kara kaimi wajen rage talauci a kasar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Murtala Adeleke, ya bayyana hakan bayan taron kungiyar da aka gudanar a Abuja. Ya ce duk da cewa gyare-gyaren tattalin arziki na bukatar hakuri, ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa al’umma, musamman wadanda ke karkara, sun amfana da romon dimokuradiyya.

Sai dai kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Tinubu, tana mai cewa an samu ci gaba a bangarorin tsaro, ilimi, samar da man fetur da tattalin arziki. Haka kuma ta yaba wa gwamnatin kan kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma inganta jin dadin jami’an tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!